Jan kati: Chelsea za ta daukaka kara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya goyi bayan Nemanja Matic

Chelsea za ta daukaka kara akan katin korar da alkalin wasa ya bai wa Nemanja Matic a lokacin wasansu da Burnley ranar Asabar da suka yi 1-1.

Alkalin wasa ya kori dan wasan mai shekaru 26, dan kasar Serbia, saboda ture Ashley Barnes da ya yi kasa bayan da Barnes din ya yi masa keta ba a busa ba.

Chelsea tana da dama zuwa Talata da karfe daya na rana agogon GMT, ta gabatar da bahasinta ga hukumar kwallon Ingila domin neman janye masa hukuncin jan katin, na dakatarwa daga wasanni uku.

Idan ba a janye hukuncin ba, Matic ba zai buga wasan karshe da Chelsean za ta yi da Tottenham na kofin Capital One ba ranar Lahadi.

Haka kuma ba zai buga wasan da za su yi ba na Premier da West Ham da Southampton.

Kociyan Chelsea Jose Mourinho shi ma ya goyi da bayan martanin da dan wasan nasa ya yi.

Ya ce ketar da Barnes ya yi masa zai iya karya shi, ya sa ya ma daina wasan kwallon kafa gaba daya, kuma ko katin gargadi ba a ba shi ba.

A kakar bana Matic ya buga wa Chelsea wasannin Premier 25 daga cikin 26, hadi da sauran wasanni ya buga sau 37.