Ingila: An ki yarda da filin wasa na roba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawancin 'yan wasa a Ingila ba sa son filin wasa mai ciyawar roba

Kungiyoyin kwallon kafa na kasa da gasar Premier ta Ingila sun yi watsi da shirin sake dawo da amfani da filayen wasa masu ciyawar roba.

An yi kankankan a kuri'ar da aka yi akan shirin a watan Nuwamba na 2014, amma kuma kungiyoyin suka sake kada kuri'a a makon da ya wuce, inda suka ki amincewa da shirin.

Mai magana da yawun kungiyoyin na gasar kasa da Premier (Football League), ya ce, yawancin kungiyoyin sun fi son wasa a fili na gaske.

Ita ma kungiyar kwararrun 'yan wasa ta Ingila ta goyi bayan matakin da cewa ya zo daidai da bukatar 'yan wasa.

Mataimakin shugaban kungiyar kwararrun 'yan wasan, Simon Barker, ya ce, wasu daga dalilan da suka sa kungiyoyi ke son amfani da filayen na ciyawar roba, ba wai saboda inganci ba ne.

Ya ce suna yin hakan ne saboda karin kudi da suke samu ne, ta hanyar bayar da hayarsu.

A shekarar 1995 ne aka hana amfani da filayen masu ciyawar roba a wasannin kwararru saboda matsalolin tafiyar kwallo da kuma rauni da 'yan wasa kan ji.

Amma kuma an yarda a yi amafani da su a wasannin cin kofin Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA da wasannin lig-lig na kasa da Premier.