Qatar 2022: A yi a Nuwamba da Disamba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Daya daga cikin filayen wasan kofin duniya na Qatar 2022

Kwamitin musamman na hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ya bayar da shawarar yin gasar ta 2022 a Qatar a watannin Nuwamba da Disamba.

Manyan jami'an kwallon kafa ne suka taru a Doha domin tattaunawa kan shawarwar saboda fargabar yin gasar a lokacin bazara, saboda zafi zai iya shafar lafiyar 'yan wasa da 'yan kallo.

Yanayin zafi a lokacin bazara a Qatar yakan wuce maki 40 a ma'aunin Celcius, yayin da a watannin Nuwamba da Disamba yakan yo kasa da maki 25 a ma'aunin na Celcius.

Ana sa ran kwamitin zartarwa na Fifa zai amince da wannan shawara da aka tsaida ranakun 19 da 20 na watan Maris a Zurich.

Mataimakin shugaban Fifa, Jim Boyce, ya ce yin gasar a wadannan watanni zai jirkita abubuwa da dama, amma ya ce tun da akwai tazarar shekara takwas mutane za su iya sake tsarin abubuwansu.