U17: Afrika ta Kudu ta fitar da Najeriya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani daga cikin wasannin Najeriya na matasa

Afrika ta Kudu ta fitar da Najeriya daga gasar cin Kofin Kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 17 da ake yi a Yamai da ci 1-0.

A minti na 26i ne 'Yan Afrika ta Kudun suka jefa kwallo a ragar Zakarun na duniya, a wasan na kusa da karshe.

Yanzu Afrika ta Kudu za ta yi wasan karshe ranar Lahadi daya ga watan Maris da kasar da za ta yi nasara a karawar da za a yi ranar Alhamis tsakanin Guinea da Mali.

A ranar Lahadin Najeriya za ta yi wasan neman matsayi na uku tsakanin wadda ta yi rashin nasara a wasan Guinea da Mali.

Kasashe hudu da suka kai wasan na kusa da karshe a Nijar din za su wakilci Afrika a gasar duniya a Chile, tsakanin 17 ga watan Oktoba da takwas ga watan Nuwamba.

Kasashe 24 ne za su fafata a gasar da za a yi a filayen wasa takwas.