U17: Guinea ta doke Najeriya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya ta yi fice a gasar matasa ta duniya

Guinea ta doke Najeriya a wasan neman matsayi na uku a gasar cin Kofin Afrika ta 'yan kasa da shekara 17 a babban birnin Nijar Yamai.

Najeriya ce ta fara jefa kwallo a ragar 'yan Guinea, daga nan suka rama kuma suka kara wa Najeriya kwallaye biyu a raga.

Afrika ta Kudu da Mali ne ke wasan karshe na gasar, wadd Najeriyar ke rike da kofinta na duniya, ko da ike daman ba ita ke rike da na Afrika ba.

Rashin nasarar ba zai hana Najeriya zuwa gasar duniya da za a yi ba a nan gaba a Chile, domin kasashe hudu da suka je wasan kusa da karshe su za su wakilci Afrika a ta duniya.