U17: Mali ta dauki kofin Afrika

Image caption Mali ta karbe kofin ke nan daga hannun Kamaru

Mali ta dauki kofin kwallon kafa na kasashen Afrika na 'yan kasa da shekara 17 bayan da ta doke Afrika ta Kudu 2-0 a Yamai.

An tafi hutun rabin lokaci ba tare da cin kwallo ba, sai bayan da aka dawo daga fili ne a wajen minti na 60 Mali ta ci kwallon farko.

'yan minti tsakani ne kuma sai 'yan wasan Malin suka kara kwallo ta biyu a ragar 'yan Afrika ta Kudun.

Kafin wasan na karshe an yi wasan Najeriya da Guinea domin neman matsayi na uku, inda aka ci Najeriya uku da daya.

Yanzu Mali ta karbe kofin gasar daga hannun Kamaru ke nan.

Dukkanin kasashe hudu da suka kai wasan kusa da karshe za su wakilci Afrika a gasar Duniya da za a yi a Chile, a ranakun 17 ga watan Oktoba zuwa takwas ga watan Nuwamba na 2015.