Wasan Commonwealth: Durban na nema

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Usain Bolt a yayin wasan Commonwelath

Kudurin birnin Durban na neman karbar bakuncin wasannin Commonwealth ya tabbata a hukumance.

Wata tawagar Afrika ta Kudu ta bayyana shirye-shiryenta a lokacin wani biki na musamman a birnin London a ranar Litinin din nan.

Kasancewar birnin shi ne daya tilo da ke neman karbar bakuncin, zai kafa tarihi na gudanar da wasannin na Commonwealth a Afrika a karon farko.

Wannan kuma zai bude damar neman karbar bakuncin wasannin Olympics a nan gaba.