Kofin Afrika: Guinea ta ki yarda

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Guinea ta ce kamata ya yi CAF ta tuntube ta kafin ta bayyana sauyin

Guinea ta ki amincewa da maganar sauya lokacin gasar Kofin Afrika ta 2023 zuwa watan Yuni saboda gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.

Ministan wasanni na Guinea Domani Dore ne ya bayyana matsayin kasar, wanda ya saba da maganar babban sakataren Fifa, Jerome Valcke.

A makon da ya wuce ne Valcke, ya ce, gasar ta Kofin Afrika, za a dawo da ita baya da wata shida, zuwa watan Yuni, daga watan Janairu da aka saba yin ta.

Valcke ya ce, yin gasar ta Afrika wata daya bayan gasar Kofin Duniya ba abu ne mai yuwuwa ba, ya kara da cewa an daidaita da hukumar kwallon kafa ta Afrika, CAF, a matsar da gasar ta Afrika zuwa gaba.

Ministan wasannin na Guinea ya ce ba za su amince da sabon lokacin da aka sa na gasar ba, saboda lokacin damuna ne.