Rooney: Angel Di Maria zai farfado

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallo uku Di Maria ya ci wa Man United a kakar bana

Kyaftin din Manchester United Wayne Rooney ya ce, dan wasansu na gaba Angel Di Maria zai farfado daga halin da yake ciki na rashin tabuka wani abu a fili.

Rooney mai shekaru 29 ya ce, ''babban dan wasa ne. Ba ka rasa baiwa da kwarewarka rana daya. Ina ganin zai gano bakin zaren.''

Ya kara da cewa,'' dole ne sai ka saba da yanayin da ka samu kanka a ciki, na tabbata zai farfado daga yanzu zuwa karshen kaka.''

Bayan da ya fara haskakawa a Old Trafford, Di Maria, mai shekara 27, wanda aka sayo daga Real Madrid a kan fan 59.7 a kwanakin nan ba shi da katabus a wasa.

An hana dan wasan sakat a karawar da Manchester United ta yi nasara a kan Sunderland ranar Asabar da ci 2-0, abin da ya sa aka sauya shi a kashi na biyu na wasan.

Kocin Manchester United Louis van Gaal na ganin akwai abin da ke damun dan wasan, bayan da a ka yi kokarin fasa gidansa a Cheshire a yi masa sata a karshen watan Janairu.

Shi kuwa tsohon dan wasan Liverpool da Fulham Danny Murphy, yana ganin wurin da Van Gaal yake sa dan wasan ne, wanda ya saba da yadda ya saba, ke shafarsa kokarinsa.