Terry:Ba zan sauya shawara kan Ingila ba

Terry ya fara yi wa Ingila wasa a watan Yuni na 2003

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Terry ya fara yi wa Ingila wasa a watan Yuni na 2003

Tsohon kyaftin din Ingila John Terry ya kawar da yuwuwar komawa buga wa Ingila wasa,amma ya yarda cewa ya rasa damar yin manyan wasanni a Wembley.

Terry wanda ya daina yi wa Ingila wasa a 2012, ya jagoranci Chelsea ta dauki kofin League(Capital One) bayan da ta doke Tottenham 2-0 ranar Lahadi.

Ya ce, ''ko alama ban taba tunanin in sake dawowa buga wa Ingila wasa ba, na rika na yanke hukunci, domin tawagar ta ci gaba.''

Terry mai shekaru 34 ya yi wa Ingila wasa sau 78 amma ya yi ritaya a 2012, lokacin da yake fuskantar tuhumar nuna wariyar launin fata daga hukumar FA, a kan Anton Ferdinand.

Duk da cewa kotu ta wanke shi amma hukumar FA ta same shi da laifi inda ta hana shi buga wasanni hudu da kuma tarar fan 220,000.

Terry ya buga wa Ingila wasansa na karshe da Moldova a watan Satumba na 2012 a wasan neman zuwa gasar kofin duniya na 2014.