Masar ta nada Cuper a matsayin koci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hector Cuper

Kasar Masar ta nada Hector Cuper na Argentina a matsayin kocin tawagar 'yan kwallonta.

Hukumar kwallon Masar ta ce an yi naddin ne sakamakon taron da aka yi karkashin jagoranci Gamal Allam.

Cuper ya jagoranci Valencia zuwa wasan karshe na gasar zakarun Turai a shekara ta 2000 da kuma 2001, sannan ya jagoranci Inter Milan ta kai matsayin na biyu a gasar Serie A a shekara ta 2003.

Tun a watan Nuwamba, Masar ba tada kocin 'yan wasan bayan ficewar Shawki Gharib.

Masar ba ta tsallake zuwa gasar cin kofin Afrika a 2015 ba, sannan rabonta da gasar cin kofin duniya tun a shekarar 1990.