An damke Johnson bisa zargin yin lalata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunderland ta dakatar da Johnson

'Yan sanda sun tsare dan kwallon Ingila da kuma Sunderland Adam Johnson bisa zargin yin lalata da yarinya 'yar shekaru 15.

'Yan sanda a Durham sun damke dan wasan mai shekaru 27 inda suka yi masa tambayoyi a caji ofis kafin su bada belinsa.

Kungiyar Sunderland ta ce ta dakatar da dan wasan har sai an kamalla bincike.

Dan wasan ya soma taka leda ne a Middlesbrough lokacin yana da shekaru 17 a shekara ta 2005.

Ya taba taka leda a Leeds United da Watford da kuma Manchester City.