Mourinho: Za a sabunta kwantiragin Terry

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption John Terry ya dauki manyan kofuna 15 a shekara 17 da ya yi a kungiyar

Kociyan Chelsea Jose Mourinho, ya ce, kungiyar za ta sabunta kwantiragin kyaftin din ta John Terry.

Kwantiragin tsohon kyaftin din na Ingila zai kare ne a karshen kakar wasanni ta bana.

Mourinho ya ce, ''ina bayar da tabbacin cewa zai kasance dan wasan Chelsea a kaka mai zuwa, babu wata tantama a kan haka.''

Dan wasan zai iya samun sabon kwantiragin shekara daya ne saboda ka'idar kungiyar ta bai wa 'yan wasan da suka wuce shekara 30 karin kwantiragin watanni 12.

An bai wa Terry kyautar gwarzon dan wasa a karawarsu da Tottenham da suka dauki kofin Capital One, bayan da ya fara cin kwallo a wasan da suka tashi 2-0, ranar Lahadi.

Terry mai shekara 34 ya buga wa Chelsea wasanni sama da 550 tun daga 1998.