Wenger: Kofin Premier ya yi mana nisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kocin ya ce, ''duk da haka za mu yi iya kokarinmu''

Kociyan Arsenal Arsene Wenger, ya ce, kofin gasar Premier ya yi musu nisa a yanzu yayin da ya rage wasanni 11 a gama.

Kungiyar tana matsayi na uku ne a tebur da tazarar maki tara tsakaninta da Chelsea ta daya.

Wenger yana ganin kofin ya yi musu nisa duk da nasarar da suka samu a wasanninsu shida daga cikin bakwai na karshe a gasar.

Sai dai duk da rashin kwarin guiwar, Wenger mai shekara 65 yana son kungiyarsa ta ci gaba da matsawa Chelsea kamar yadda Man City ta yi wa Man United a kakar 2011-12 ta dauki kofin.

Haka kuma Wenger ya ce bai ga dalilin da Manchester City za ta karaya ba kan cin kofin na Premier a bana, yana mai cewa ta yi hakan shekaru uku da suka wuce, da tazarar maki 8 a lokacin.

Dan wasan Arsenal din Aaron Ramsey ya murmure daga jinyar da ya yi kuma zai buga wasansu da QPR a ranar Laraba