Tottenham na son Kane ya bar gasar U21

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pochettino- Akwai bukatar mu tattauna da dan wasan da kuma FA

Kociyan Tottenham Mauricio Pocettino yana shirin ganawa da hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, don ta bar dan wasansu Harry Kane ya huta.

Kociyan yana ganin Ingila za ta gayyaci Kane mai shekara 21 domin gasar kofin Turai ta 'yan kasa da shekara 21, wanda hakan zai sa dan wasan ya gaji.

A kakar wasan bana Kane ya yi wa Tottenham wasanni 39, inda ya ci kwallo 24.

Pochettino ya ce, ''watakila zan so Harry ya samu hutun wata daya bayan kakar wasannin, domin ya samu hutu da natsuwa.''

Kocin ya ce, '' wannan ra'ayina ne, amma na san akwai bukatar mu goya wa tawagar wasan kasa baya, kuma mu yanke shawara mafi kyau gare mu baki daya, wannan ita ce damuwarmu domin dan wasanmu ne.

Ya zuwa yanzu Kane bai samu gayyatar yi wa babbar kungiyar Ingila wasa ba, amma ana ganin Roy Hodgson ya gayyace shi domin wasansu da Lithuania da Italiya nan gaba a watan nan.