Senegal ta nada Cisse a matsayin koci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai kalubale da dama a kan Aliou Cisse

Senegal ta nada tsohon dan wasanta Aliou Cisse a matsayin kocin tawagar 'yan kwallonta watau Teranga Lions.

Dan shekaru 38, ya buga wa Senegal wasanni 35 kuma ya kulla yarjejeniya ta shekaru hudu domin jan ragamar tawagar 'yan kwallon kasar.

Ya maye gurbin Alan Giresse wanda ya ajiye aiki bayan kamalla gasar cin kofin Afrika a bana.

Cisse ya kasance mataimakin kocin tawagar 'yan kwallon Senegal lokacin gasar Olympics a shekara ta 2012.

A lokacin yake taka leda, ya buga wa kungiyoyin Lille da Paris Saint-Germain da Montpellier bda Birmingham City da kuma Portsmouth.