Barcelona ta zama jagaba a La Liga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau 32 Messi ya ci wa Barcelona kwallaye uku-uku a wasa (hat-trick)

Barcelona ta karbe ragamar La Liga daga Real Madrid bayan da ta lallasa Rayo Vallecano da ci 6-1 a Camp Nou.

Minti biyar da sa wasa Suarez ya fara jefa kwallo a ragar bakin kafin Pique shi ma ya ci a minti na 49.

Sai kuma Messi wanda ya ci uku a jere, wanda wannan ne karo na 24 da ya ci wa kungiyarsa kwallaye uku-uku (hat-trick) a La Liga, ya ci kwallon farko ne da fanareti a minti na 56, sai ta biyu a minti na 63, bayan minti biyar kuma ya kara ta uku.

Rayo Vallecano ta 11 a tebur da maki 29, ta ci kwallonta daya da fanareti ta hannun Bueno, kafin kuma Suarez ya kar cinsu tasa ta biyu ta shidan Barcelona ana dab da tashi bayn minti 90.

Yanzu Barcelona ta zama ta daya a tebur da maki 62 a wasanni 26 da yawan kwallaye 60, yayin da Real Madrid wadda Athletic Club ta ci 1-0 ranar Asabar ta koma ta biyu.

Real Madrid tana da maki 61 da kwallaye 51 a wasanni 26, yayin da Atletico Madrid ke matsayi a uku da maki 54 da kwallaye 28 amma a wasanni 25.

A ranar Lahadin nan Atletico da ta karbi bakuncin Valencia, sun tashi kunnen doki daya da daya da hakan ya sa Valencia ta ci gaba da zama a matsayi na hudu da maki 54, Valencia kuma ta biyar da maki 53.