Brazil: Filin wasa ya zama tashar mota

Hakkin mallakar hoto Portal da Copa
Image caption Kusan motocin safa 400 ake ajiye wa kullum a filin wasan

An mayar da daya daga cikin manyan filayen da aka yi gasar cin Kofin Duniya a Brazil a 2014 wurin ajiyar motoci saboda rashin manyan kungiyoyin wasa.

Saboda babu manyan kungiyoyin wasan kwallon kafa a babban birnin kasar ta Brazil, wato Brasilia, wadanda ake da su a birnin ba sa jawo 'yan kallo da suka wuce 10,000.

A shekaran nan ta 2015 wasannin sada zumunta biyu kawai aka yi a filin na Estadio Mane Garrincha wanda yake daukar 'yan kallo 72,000.

Filin wasan, wanda aka kashe kusan fan miliyan 350 an yi kiyasin in ban da filin Wemley na Ingila ba wanda ya fi shi tsada.

Saboda kudin da ake kashewa wurin kula da filin, fan 130,000 a duk wata, ya sa aka bullo da dabarar amfani da filin a matsayin wata tashar motacin safa na birnin na Brasilia.

Kusan motoci 400 ake ajiye wa a filin kowace rana, yayin da hukumomi kuma ke amfani da ofisoshin filin wasan wajen gudanar da ayyukansu.