Kofin FA: Blackburn ta rike Liverpool

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Karon farko da Liverpool ke fafatawa a kofin FA ke nan tun 2006

Blackburn Rovers ta tayar wa da Liverpool hankali a karawar da suka tashi 0-0 da ta tilasta sai an sake wasansu na dab da na kusa da karshe na cin Kofin FA.

Wannan shi ne karon farko da Liverpool ke fafutukar neman daukar kofin na FA tun 2006

Raunin da kyaftin din Liverpool Steven Gerrad yake jiyya tsawon wasanni shida ya hana shi damar buga wasansa na karshe na FA a Anfield.

Sai dai kyaftin din na fatan buga wasan karshe na kofin ranar 30 ga watan Mayu, idan har sun kai.

Gerrard ya dauki kofin na FA sau biyu da Liverpool, kuma wasan karshe na wannan shekara za a yi shi ne a ranar dan wasan ke cika shekara 35.

An dakatar da wasan tsawon minti takwas saboda Martin Skrtel dan wasan baya na Liverpool ya ji rauni a ka bayan da suka hadu daRudy Gestede.