U20: Nigeria ta doke Senegal 3-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe hudu na farko a gasar za su wakilci Afrika a gasar duniya

Najeriya ta zama ta farko a rukuni na daya,Group A, a gasar cin Kofin Afrika ta 'yan kasa da shekara 20, bayan ta doke Senegal 3-1.

Awoniyi Taiwo Micheal shi ne ya ci wa Najeriya kwallon farko da ta biyu, kafin Sidy Sarr ya rama wa Senegal din mai masaukin baki daya.

Ifeanyi Mathew shi ne ya kara ci wa Najeriya mai rike da kofin gasar kwallonta ta uku.

Yanzu Najeriya tana da maki uku da bambancin kwallaye biyu a wasa daya.

Wasa tsakanin Congo da Ivory Coast su ma a rukunin na daya an tashi daya da daya.

Najeriya za ta yi wasanta na gaba ranar 11 ga watan nan na Maris da Congo.

A ranar Litinin din nan 9 ga watan Maris za a yi wasannin rukuni na biyu tsakanin Afrika ta Kudu da Ghana, da kuma tsakanin Zambia da Mali.