Van Gaal: Ban damu da kofin FA ba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kofin FA ba zuwa gasar Zakarun Turai ba shi da amfani inji van Gaal

Kociyan Manchester United Louis van Gaal, ya ce samun matsayi na daya zuwa hudu a Premier ya fi daukar kofin FA a wurinsa.

A ranar Litinin Man United za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan dab da na kusa da karshe(quarter final) na kofin hukumar kwallon Ingila, FA.

Van Gaal, ya ce, ''kammala Premier a jerin hudun farko, kyakkyawan sakamako ne, kuma mu a Manchester ba karamin abu ba ne a garemu.''

Kociyan ya kara da cewa, ''idan ka ci kofin FA ba za ka je gasar Zakarun Turai ba, ka dai dauki kofi ne kawai.''

Van Gaal, ya ce, ''ina ganin Wenger, ya yi gaskiya da yake cewa babban matsayi da kungiya za ta samu shi ne ta kai wasan Kofin Zakarun Turai.''

A yanzu Manchester United tana bayan Arsenal ta uku a tebur, a matsayi na hudu da bambancin maki daya.

Bayan haduwarsu da Arsenal ta kofin na FA ranar Litinin, United za ta kara da Tottenham da Liverpool da Aston Villa da kuma Manchester City a Premier.