Arsenal ta doke Man United 2-1

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Welbeck ya yanke De Gea zai ci kwallo ta biyu

Danny Welbeck ya ci kwallon da ta yi waje da tsohuwar kungiyarsa Man United daga gasar kofin FA, kuma ta kai Arsenal wasan kusa da karshe.

Dan wasan bayan Arsenal Nacho Monreal ne ya fara daga ragar Manchester United minti 25 da wasa.

Minti hudu tsakani ne kuma sai Wayne Rooney ya rama wa United.

Kuskuren da Antonio Valencia ya yi ne na turawa David De Gea kwallo baya ya sa Welbeck ya samu kwallon ya yanke mai tsaron ragar ya sheka ta a raga.

A minti na 77 alkalin wasa ya kori Angel Di Maria bayan ya fadi da gangan an ba shi katin gargadi(yellow), sai ya ja rigar alkalin wasan ta baya, lamarin da ya sa ya kara masa katin na biyu, ya kore shi.

Arsenal za ta kara a wasan kusa da karshe da tsakanin Bradfor da Reading)wadda ta yi nasara).

A daya wasan na kusa da karshe kuwa Aston Villa za ta kara da tsakanin Liverpool da Blackburn