Cagliari ta kori Zola

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Zola ya kare wasansa ne a kungiyar

An kori Gianfranco Zola a matsayin kociyan Cagliari bayan wasanni goma kacal da ya jagoranci kungiyar ta Serie A.

A watan Disamba aka dauki tsohon dan wasan na Chelsea aikin, inda ya kai su samun maki takwas daga cikin 30.

Doke su 2-0 da Sampdoria ta yi, ya sa kungiyar ta 18 a tebur, ta zama ta ukun karshe, inda maki hudu ke tsakaninta da kauce wa faduwa daga Serie A.

A sanarwar da kungiyar ta fitar kan sauke shi daga aikin, ta nuna damuwa kan matakin da ta ce ta dauka kan mutumin da ya kafa mata tarihin da ba za a manta da shi ba.

Zola wanda ya yi ritaya daga wasa a kungiyar ta Cagliari a 2005, ya yi shekara bakwai a Chelsea tsakanin 1996 da 2003.

Mai shekara 48 ya fara aikin kociya a West Ham a 2008, amma a ka kore shi a 2010, kasa da shekara biyu da fara aiki, kafin kuma ya ajiye aiki bayan shekara daya da Watford a 2012.