FA: Jadawalin wasannin kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa ce kadai ta fito daga cikin kungiyoyi hudu na wasan kusa da karshe

A ranar Litinin din nan za a yi jadawalin wasannin kusa da karshe na Kofin hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA.

Ya zuwa yanzu kungiyar Aston Villa ce kadai ta samu gurbi a matakin na kungiyoyi hudu, bayan da ta yi nasara a kan West Brom 2-0.

Canjasar 0-0 da Liverpool ta yi da Blackburn ya sa dukkaninsu sun zama kamar Bradford da Reading da su ma suka tashi 0-0.

Za a fitar da jadawalin ne bayan wasan Manchester United da Arsenal a Old Trafford.

Tsohon mai tsaron ragar Man United Peter Schmeichel da mai gabatar da shirye -shirye na BBC Dermot O'Leary su za su jagorancin bikin.

Za a yi wasannin na kusa da karshe ne a ranar 18 da 19 na Afrilu.

A ranar Litinin 16 ga watan Maris za a sake wasan dab da na kusa da karshe na Reading da Bradford, na Blackburn da Liverpool kuwa har yanzu ba a sa rana ba.