Van Gaal na bukatar shekaru biyu zuwa uku

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Van Gaal na fuskantar matsin lamba

Tsohon kyaftin din Manchester United, Roy Keane ya ce zai zama "bala'i" idan kungiyar ta kasa shiga rukunin kungiyoyi hudu na farko a gasar Premier ta Ingila.

A cewarsa, kocin tawagar Louis van Gaal na bukatar karin shekaru biyu zuwa uku domin sake farfado da tawagar.

Bisa dukkan alamu United ba za ta lashe kowanne kofi ba a shekara ta biyu a jere, bayan da Arsenal ta doke ta da ci biyu da daya a gasar cin kofin FA.

"A baiwa mutumin shekaru biyu zuwa uku," in ji Keane.

Ya kara da cewa "Van Gaal zai sha suka amma kuma hakan ba sabon abu bane."

A yanzu United ce ta hudu a teburin gasar Premier amma a sauran wasanninta 10 za ta hadu da Liverpool,Manchester City,Chelsea da kuma Arsenal.