Van Gaal: Di Maria ba shi da ta cewa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Na yi magana da shi ya kuma san ra'ayina, amma zan kalli bidiyon lamarin, in ji Van Gaal

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce, Angel Di Maria ba shi da wani dalili na sa wa alkalin wasa ya kore shi a wasansu da Arsenal.

Alkalin wasa ya kori dan wasan dan Argentina mai shekar 27, sakakon katin gargadi biyu da ya ba shi a kusan lokaci daya.

Na farko sakamakon faduwa da alkalin wasa ya ce ya yi da gangan don neman fanareti, sannan kuma sakamakon hatsaniyar hakan, ya ja rigar alkalin wasan ta baya,lamarin da ya sa alkalin ya kore shi.

Van Gaal, ya ce, ''ina jin ya taba alkalin wasan, wanda hakan ba daidai ba ne a kowace kasa, sboda haka ba shi da ta cewa.''

Kocin ya kara da cewa, ''a Spain, ya san cewa ba zai taba alkalin wasa ba, to amma yana cikin bacin rai ne.''

Arsenal ta fitar da Manchester United daga gasar ta kofin FA da ci biyu da daya a Old Trafford, ta kai wasan kusa da karshe.