Mourinho: PSG ce ta fi ba mu wahala

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mourinho ya ce, '' duk kungiyar da take daga Ingila ba za ta damu da matsi ba, domin matsi yana kasarmu.''

Kociyan Chelsea, Jose Mourinho, ya ce, Paris St-Germain, ita ce kungiya mafi matsin lamba da suka kara da ita a bana.

Kociyan ya ce, '' a bana mun yi wasa da kungiyoyi daga gasar da ke bin Premier wato Championship da mai bi mata ta League One da kuma ta bayanta League two, amma wadda ta fi matsa mana ita ce PSG. Daman ina tsammanin haka daga kungiyar da ke da 'yan wasa kwararru da yawa.'' Amma kuma duk da wannan bayani na Mourinho, ya ce za su yi nasara.

A wasan dab da na kusa da karshe da suka yi na bara Chelsea ta yi galaba a kan PSG wadda ta ci ta 3-1 a Paris, da ci 2-0 a London, sakamakon fifikon cin kwallo a waje.

A haduwar da za su yi ranar Larabar nan a London ta matakin 'yan 16 bayan wadda suka yi a makon da ya wuce a Paris wadda suka tashi 1-1, kocin PSG Laurent Blanc, na ganin Zlatan Ibrahimovic zai whalar da 'yan wasan bayan Chelsea.

Haka kuma kociyan na PSG ya gargadi 'yan wasansa da su yi hankali da Diego Costa na Chelsea, wanda ya ce yana harzuka 'yan wasa.

A lokacin wasan na Larabar nan 'yan wasan PSG za su daura bakin kyalle a hannunsu, domin alhinin mutuwar 'yan kasar Faransa takwas da suka hada da fitattun 'yan wasa uku da suka mutu a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a Argentina ranar Litinin.