Neymar:'Yan gaban Barca sun fi na Real

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Neymar, dan wasan Bercelona

Dan wasan Barcelona Neymar ya ce 'yan wasan gaba na kungiyarsu sun fi na Real Madrid kyau.

'Yan wasan gaba na Barca sun hada da shi Neymar da Suarez da kuma Messi.

Ita kuwa Real Madrid tana da Ronaldo da Gareth Bale da kuma Benzema.

Neymar ya kuma ce kungiyar za ta iya maimaita bajintar da ta yi ta daukar kofuna uku a bana ma.

A yanzu dai kungiyar na fafutukar daukar kofin La Liga da na Zakarun Turai da kuma Copa del Rey.