Kasar Qatar za ta dawo Ingila wasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Qatar ce ta 109 a jerin gwanayen kwallon kafa a duniya, mataki 58 tsakaninta da Ireland ta Arewa

Kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Qatar za ta yi amfani da filin wasan hukumar kwallon Ingila da ke St George Park domin wasanninta na sada zumunta da kungiyoyin Turai a watan Mayu.

Hukumar ta FA, ta ce an yi wannan tsari ne na bai wa kasar Larabawan wannan dama bisa yarjejeniyar kasuwanci, kamar yadda aka taba yi da Barcelona da Galatasaray da kungiyar kasar Montserrat.

Kungiyar ta kasa ta Qatar za ta yi atisaye a filin wasan na FA da ke Burton a shirin wasansu da Ireland ta Arewa da za su yi a wani filin wasa da ba a sanar ba a tsakiyar London rnar 31 g watan Mayu.

Shugaban hukumar kwallon ta Ingila Greg Dyke ya yi adawa da bai wa Qatar damar karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2022.

Qatar ita ce ta 109 a jerin gwanayen kwallon kafa a duniya, mataki 58 tsakaninta da Ireland ta Arewa.