Perez: Bale da Ancelloti na nan daram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rashin cin kwallo a bana ya harzuka magoya bayan Real Madrid din a kan Bale da Ancelotti

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya goyi bayan ci gaba da zaman Gareth Bale, ya kuma musanta maganar korar Ancelotti.

Perez ya ce, ko menene ya faru a cikin kwanaki ko makonnin da ke tafe Carlo Ancelotti zai cigaba da zama kocin Real Madrid.

Game da Gareth Bale kuwa, ya ce dan wasa ne na duniya, wanda manyan kungiyoyi ke son sa.

Shugaban ya bai wa magoya bayan kungiyar hakuri a kan dan wasan da kociyan, yana mai cewa su duba abin da Bale ya yi a kungiyar a shekararsa ta farko.

Perez ya bayyana matsayin kungiyar ne a wani taron manema labarai na gaggawa da ya kirawo sakamakon jita-jitar da ake yadawa cewa za a kori Ancelotti.

Perez ya sayo Bale daga Tottenham a kan kudin da ba su taba kashewa ba wurin sayen dan wasa fam miliyan 85 a watan Satumba na 2013.

Gareth Bale mai shekara 25, dan Wales, a kakarsa ta farko a kungiyar ya ci kwallo 22, amma yanzu a wasanni tara bai ci ko da kwallo daya ba.

Haka kuma magoya bayan kungiyar sun soke shi a lokacin wasansu na ranar Talata da Schalke ta ci su 4-3 duk da cewa Real din ta yi galaba da ci 5-4 wasa gida da waje.

Barcelona ta doke Zakarun na Turai daga matsayi na daya a La Liga, kuma magoya bayansu sun rika yi musu ihu, a wasansu na gasar Zakarun Turan na ranar Talata.

To sai dai kuma kociyan Isra'ila Eli Guttman ya ce Bale din yana tsimin kansa ne domin wasan Wales da Isra'ilan, na neman zuwa gasar kofin Turai ta 2016.

A ranar 28 ga watan Maris Isra'ila za ta karbi bakuncin Wales a wasan, kuma Guttman ya ce dan wasan ya fi damuwa da kasarsa a kan kungiyarsa.