Mayweather: Ban shirya shan kaye ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bieber da Mayweather da Pacquiao a shirin damben boksin mafi tsada a kallo a tarihi

Floyd Mayweather ya gaya wa abokin karawarsa a damben boksin din da za su yi ranar 2 ga watan Mayu, Manny Pacquiao cewa bai shirya shan kashi ba.

Mayweather mai shekara 38, wanda ya yi nasara a dukkanin dambensa 47, ya gaya wa Pacquiao hakan ne a wani taron manema labarai a Los Angeles ranar Laraba.

Ya kara da cewa, '' ranar 2 ga Mayu, duniya za ta tsaya cik, a lokacin babban damben boksin a tarihi, na Mayweather da Pacquiao.'' in ji ba'amurken.

Tun da farko yayin taron manema labaran kusan 700, Manny Pacquiao mai shekara 36, wanda ya yi nasara a dambensa 57, da canjaras biyu, sannan aka doke shi sau biyar, ya ce zai doke Mayweather domin amfanin damben.

Pacquiao dan kasar Philippines, ya fadi hakan ne, dangane da yadda yake ganin abokin karawar tasa, yana rayuwa ta almubazzaranci da dukiyar da yake samu, inda ya ce hakan ba daidai ba ne ga sana'ar damben boksin.

An yi kiyasin tikitin kallon wasan zai kai tsakanin dala 1500 zuwa 7500 kwatankwacin naira dubu 330 zuwa miliyan daya da dubu 650.

Duk da tsadar tikitin ana ma ganin ba za a sa shi ne a kasuwa ba ta yadda duk mai so da kuma hali zai iya saya, domin ana sa ran fitattun mutane ne za su cika dandalin da za a yi damben na MGM Grand Garden Arena a Las Vegas, a Amurka.