Zakarun Turai: PSG ta yi waje da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty

Paris St Germain ta fitar da Chelsea daga gasar Zakarun Turai bayan sun tashi 2-2 a Stanford Bridge, a kan tasirin kwallon waje.

A wasansu na farko a Paris sun tashi daya da daya ne.

A wasan da aka yi cikin minti 90 sun yi kunnen doki 1-1.

Gary Cahill ya fara ci wa Chelsea kwallonta a minti na 81 bayan da ya yi kwance-kwance ya shimfido kwallon.

Minti hudu tsakani ne kuma tsohon dan wasan Chelsean David Luiz ya rama da ka.

Bayan mintina 90 aka shiga karin lokaci na minti 30 inda Chelsea ta samu fanareti Hazard ya ci a minti na 96.

Bayan an juya ragowar minti 15 ne kuma an kusa tashi sai kyaftin din PSG Thiago Silva, wanda ya jawo musu fanaretin da Hazarda ya ci bayan ya taba kwallo da hannu, ya rama musu da ka a minti na 114.

Yanzu Paris St Germain ta tafi wasan dab da na kusa da karshe.

Tun a kashin farko na wasan alkalin wasa ya kori Ibrahimovic saboda ya yi wa Oscar keta.

A daya wasan na Zakarun Turai Bayern Munich ta kai wasan dab da na kusa da karshen a karo na hudu a jere.

Ta samu wannan dama ce bayan da lallasa Shakatar Donetsk 7-0.

A karawarsu ta farko sun tashi canjaras ne ba ci.