Europa: Everton ta doke Dynamo Kiev 2-1

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Fanaretin da Lukaku ya ci ce ta bai wa Everton nasara

Everton ta yi nasara a kan kungiyar Dynamo Kiev da ci 2-1 a wasansu na farko na kungiyoyi 16 na kofin Europa.

Oleh Gusev ne ya fara jefa kwallo a ragar Everton a minti na 14 da wasa.

Steven Naismith ya rama wa mai masauki a minti na 39, kafin Lukaku kuma ya kara ci musu da fanareti a minti na 82, bayan da Danilo Silva ya taba kwallon da hannu.

Sakamakon sauran wasannin na daren Alhamis;

Zenit St P 2 - 0 Torino ;Club Brugge 2 - 1 Besiktas ;Dnipro Dnipropetrovsk 1 - 0 Ajax ; Fiorentina 1 - 1 Roma

Napoli 3 - 1 Dinamo Moscow ;Villarreal 1 - 3 Sevilla ; Wolfsburg 3 - 1 Inter Milan

A mako mai zuwa ranar Alhamis 19 ga watan Maris za a yi karo na biyu na wasannin.