An sallami 'yan wasan Kano Pillars biyu daga asibiti

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Page
Image caption Yanzu dai dan wasa, Gambo Muhammad ne ke ci gaba da jinya.

An sallami 'yan wasan Kano Pillars biyu daga asibiti bayan jinyar da suka yi sakamakon fashin da aka yi musu.

'Yan wasan da aka sallama su ne Eneji Otekpa da Murtala Adamu.

A makon jiya ne 'yan fashi suka harbi 'yan wasa biyar na kungiyar, wandanda suka hada da Gambo Mohammed da Ogbonaya da Eneji Otekpa da Murtala Adamu da kuma Moses Ekpai a garin Abaji da ke Abuja.

Suna kan hanyarsu ne ta zuwa Owerri domin karawa da Heratland a gasar Premier bana wasan farko.

Sai dai ba a kwantar da Ogbonaya da Moses Ekpai ba domin ba su samu raunuka masu tsanani ba.

Yanzu dai dan wasa, Gambo Muhammad ne ya rage wanda har yanzu yake yin jinya.