Arsene Wenger: Za mu iya doke Monaco

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal na fatan kai wa zagayen gaba a Kofin Zakarun Turai

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce za su iya fitar da Monaco daga gasar Kofin Zakarun Turai, duk da doke su 3-1 da aka yi a wasan farko.

Wenger ya kara da cewar suna fuskantar kalubale a karawar, amma zai yi kokari su kai wasan zagayen gaba a gasar.

Haka kuma kocin ya ce masu hasashe na hangen Arsenal sai dai ta tara a gasar badi, amma hakan zai iya sauya wa ta yadda za su tunkari fafatawar.

Ranar Talata ne Arsenal za ta ziyarci Monaco a Faransa, wacce ta samu nasara a karawar farko da ci 3-1 a Emirates.