'Di Maria zai ci gaba da wasa a United'

Angel Di Maria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Di Maria ya koma United kan kudi sama da fam miliyan 59 a bara

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce, Angel Di Maria zai ci gaba da buga wa kulob din wasanni a badi.

Di Maria wanda United ta sayo a bara, ana rade-radin zai iya barin kulob din ganin baya kan ganiyarsa da kuma jan kati da aka ba shi a wasa da Arsenal a kofin FA.

Dan wasan wanda ya koma United a Agustan bara, rabonsa da ya ci kwallo tun 1 ga watan Disamba.

Van Gaal wanda ke shan suka kan salon koyar da wasansa ya ce yana fatan zai karasa shekaru uku na kwantaraginsa da United.

Ranar Lahadi United za ta karbi bakuncin Tottenham a gasar Premier wasan mako na 29 a Old Trafford.