Senegal za ta karbi bakuncin gasar matasa

Macky Sall
Image caption Tun farko Senegal tana rukuni da Zimbabwe da Swaziland ko kuma Afirka ta Kudu

Senegal ta amince da tayin da hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta yi mata na karbar bakuncin gasar matasa 'yan kasa da shekaru 23 ta Afirka.

CAF ta yi wa Senegal tayin ne domin maye gurbin Jamhuriyar Congo, wacce tace za ta mayar da hankalinta kan zaben kasar da za ta yi a shekarar 2016.

Haka kuma CAF tace gasar da za a fafata daga 5 zuwa 19 ga watan Disamba, za ta fitar da kasashen da za su wakilci Nahiyar a wasan Olympics a Rio a shekarar 2016.

Senegal wadda ke karbar bakuncin wasannin matasa 'yan kasa da shekaru 20 a bana, ta samu yabo daga shugaban CAF Issa Hayatou.