Zan dawo da tagomashi na — Adebayor

Emmanuel Adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption kwallaye biyu kacal Adebayor ya ci a gasar wasannin bana

Dan wasan Tottenham, Emmanuel Adebayor, ya ce zai kara kaimi domin ya dawo da tagomashinsa, bayan da ya shawo kan matsalolin da suka dame shi.

Dan kwallon ya ce "Na gamu da kalubale da ya shafi iyalina, amma yanzu komai ya wuce, na kuma dawo fili domin ci gaba da murza leda".

Rabon da Adebayor mai shekaru 31, ya buga wa Tottenham kallo watanni biyu da suka wuce, amma ya buga wa kulob din karawar da United ta doke su 3-1 a gasar Premier.

Dan wasan ya buga wa Tottenham wasanni 16 a bana, a inda ya zura kwallaye biyu a raga.