Hull City za ta iya sake neman sauya sunanta

Hull City Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hull City tana mataki na 15 a teburin gasar Premier

An shaida wa Hull City cewar za ta iya sake mika bukatar sauya suna zuwa Hull Tigers a kakar wasan badi.

Kungiyar ta yi kokarin canja suna ne a Afirilun bara, amma hukumar kwallon kafar Ingila ta ki amincewa da bukatar yin hakan.

Shugaban kungiyar Assem Allam, ya ce ba zai ci gaba da zuba hannun jari ba idan har aka ki amincewa da shirinsa na sauya wa kungiyar suna ba.

Allam mai shekaru 75 da haihuwa, wanda ya karbi ragamar Hull City a shekarar 2010, ya ce ya yi amanna da cewar sauya sunan zai kara martabar kungiyar da kuma bude kafar kasuwanci.