Ben Foster zai yi jinyar mako hudu

Ben Foster Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ben Foster zai yi jinyar mako hudu kuma Boaz Myhill zai maye gurbinsa

Dan wasan West Bromwich Albion Ben Foster, zai yi jinyar mako hudu bayan da ya ji rauni a gwiwarsa.

Dan wasan Ingila, mai shekaru 31, ya ji raunin ne a lokacin da suka kara da Stoke City a gasar Premier ranar Asabar.

Sakamakon jinyar da Foster zai yi ba zai buga fafatawar da kulob dinsa zai yi da Manchester City da QPR da kuma Leicester City ba.

West Brom ta maye gurbinsa da Boaz Myhill kuma shi ne ma zai shiga raga a karawar da za suyi da Manchester City a Ettihad ranar Asabar