Liverpool zai zama na biyu a Premier ta bana

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Liverpool tana mataki na biyar a teburin Premier da maki 54

Kociyan Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce kwazon kulob din da yake yi a Premier zai sa ya kammala gasar bana a matsayi na biyu

Kulob din dai ya doke Swansea da ci daya mai ban haushi ranar Litinin, kuma nasarar wasa na biyar da ya lashe a jere ke nan.

Da wannan nasarar Liverpool na mataki na biyar a teburin Premier, yayin da kulob din Manchester City, mai matsayi na biyu a teburin, ya ba shi tazarar maki hudu tsakaninsu.

Rodgers ya ce "Doke Manchester City da kulob din Hull ya yi a karshen mako shi ne ya ba su karfin gwiwar cewar za su kare a matsayi na biyu a teburin Premier bana".

Kulob din Liverpool zai karbi bakuncin Manchester United a gasar Premier wasan mako na 30 ranar Lahadi a Anfield.