'Za mu iya doke Barcelona a kofin Turai'

Pablo Zabaleta Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A wasan farko a Ettihad 2-1 aka doke Manchester City

Mai tsaron bayan kulob din Manchester City Pablo Zabaleta, ya ce za su iya fitar da Barcelona a gasar kofin Zakarun Turai ranar Laraba.

Zabaleta ya ce "Karawar ba za ta zo musu cikin sauki ba, amma sun shirya wa wasan, za kuma su yi iya kokarinsu"

Dan wasan ya bayar da misali a wasan Madrid da Schalke da kuma karawa tsakanin Chelsea da PSG, inda ya ce kwallon kafa ba ta da tabbas.

Ranar Laraba ne Barcelona za ta karbi bakuncin Manchester City, wacce aka doke 2-1 a wasan farko da suka buga a Ettihad.