FA ta tuhumi Hull City da ta da yamutsi

Hull City Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hull tana matsayi na 15 a kan teburin Premier

Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Hull City, saboda kasa tsawatar wa 'yan wasanta a lokacin da suka tashi wasa babu ci da Leicester a gasar Premier ranar Asabar.

Tuhumar ta biyo baya ne saboda 'yan wasa sun kasa tsai da hankalinsu, har ma suka zagaye alkalin wasa Jonathan Moss lokacin da ya bai wa dan wasan Hull, Alex Bruce, katin gargadi.

Daga baya ne kuma aka bai wa dan kwallon Hull Tom Huddlestone jan kati, bayan da alkalin wasa ya samu dan kwallon da yin keta a karo na biyu.

An bai wa kulob din daga nan zuwa Litinin dama, domin ya kare kansa daga tuhumar da ake yi masa.