An fitar da Dolphins a kofin Confederation

Dolphins United
Image caption Dolphins za ta dawo gida domin fuskantar wasannin Premier Nigeria

An cire kungiyar kwallon kafa ta Dolphins ta Nigeria daga gasar kofin zakarun Afirka wato Confederation Cup ta bana.

CAF ta fitar da kulob din ne sakamakon kasa isa kan lokaci domin karawar da ya kamata su yi da Club Africain na Tunisia.

Dolphins ta makara zuwa Tunisia ne sakamakon boren da 'yan wasanta suka yi a filin jirgin sama na Port Harcourt kan ladan da za a bai wa 'yan wasa, sannan ba ta bukaci CAF ta dage mata wasan ba.

Tun farko kulob din ya amince zai bai wa kowanne dan wasa kudi dala 750, a inda suka bukaci karin ladan dala 500, dalilin da ya sa suka kasa zuwa Tunisia kan lokaci.