An dage wasu wasannin Premier Nigeria

Kano Pillars Player Hakkin mallakar hoto LMC twitter
Image caption Kano Pillars za ta kara a gasar kofin zakarun Afirka a karshen mako

Hukumar gudanar da gasar Premier ta Nigeria LMC ta dage karawa tsakanin Abia Warriors da Dolphins da aka shirya za su kara ranar Alhamis.

LMC ta dage wasan mako na biyu ne a gasar Premier saboda kungiyar Dolphins har yanzu tana Tunisia domin karawa da Club Africain a gasar kofin zakarun Afirka.

Haka kuma hukumar ta ce wasan mako na uku tsakanin Dolphins da Warri Wolves da aka shirya tun farko za su kara a karshen mako shi ma za a tsayar da ranar da za a buga karawar.

A dai wasannin mako na ukun da za a kara a karshen makonnan, an dakatar da wasa tsakanin Shooting Stars da Kano Pillars domin Pillars din ta samu damar karawa a gasar cin kofin zakarun Afirka.

Sakamakon haka Sharks za ta kara da Akwa United a filin wasa na Liberation dake Port Harcourt ranar 22 ga watan Maris, sai dai sauran wasannin na nan kamar yadda aka tsara tun farko.

Wasannin mako na uku da za a kara

Enyimba Int'l FC vs Bayelsa United FC FC Taraba vs Lobi Stars FC Sharks FC vs Akwa United FC Gabros Int'l FC vs Rangers Int'l FC Giwa FC vs Sunshine Stars FC El-Kanemi Warriors FC vs Abia Warriors FC Wikki Tourists FC vs Kwara United FC Heartland FC vs Nasarawa United FC