Barcelona ta zura wa Madrid kwallaye 2-1

Barceona vs Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona wacce ke mataki na daya a teburin La Liga ta bai wa Madrid tazarar maki hudu

Barcelona ta doke Real Madrid da ci biyu da daya a gasar La Ligar Spaniya wasan mako na 28 da suka fafata a wasan Hamayya a jiya Lahadi.

Mathieu ne ya fara ci wa Barcelona kwallo a minti na 19 da fara wasa, Real Madrid ta farke kwallo ta hannun Ronaldo a minti na 31.

Daga baya ne Suarez ya ci wa Barca kwallo ta biyu a minti 56.

Da wannan nasarar Barcelona ta ci gaba da zama a matsayi na daya a Teburin La Liga da maki 68, yayin da Madrid ke matsayi na biyu da maki 64.