Man United ta doke Liverpool a Anfield

Liverpool Man United Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Manchester United tana matsayinta na hudu a teburin Premier

Manchester United ta ci gaba da zama a matsayi na hudu a teburin Premier, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-1 a Anfield ranar Lahadi.

Mata ne ya fara zuwa kwallo a ragar Liverpool a minti na 14 da fara wasa, bayan da aka dawo daga hutu ya kara ta biyu, yayin da Sturridge ya farke kwallo daya a minti na 69.

An bai wa kyaftin din Liverpool Steven Gerrard wanda ya canji Lalana jan kati a sakwan 48 da ya shiga wasan, sakamakon ketar da ya yiwa Ander Herrera.

United tana matakinta na hudu a teburin Premier da maki 59, yayin da Liverpool tana matsayinta na biyar da maki 54.