Enyimba zai kara da Bayelsa United

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Wasannin mako na uku da za a fafata ranar Lahadi

Kulob din Enyimba zai karbi bakuncin Bayelsa United a gasar Premier ta Nigeria wasan mako na uku a garin Aba.

Enyimba ya hada maki biyu daga cikin wasanni biyu da ya buga, yayin da Bayelsa United ya yi rashin nasara a wasa daya ya kuma samu maki daya a wasanni biyun da ya yi.

Sauran wasannin da za a buga kulob din FC Taraba zai karbi bakunc Lobi Stars, Enugu Rangers zai ziyarci Gabros United. Giwa FC zai fafata da Sunshine Stars na Akure, El-Kanemi Warriors da Abia Warriors za su kara a garin Kano da kuma wasan hamayya tsakanin Heartland da Nasarawa United.

Ga wasannin da za a buga a gasar Premier ta Nigeria

Enyimba vs Bayelsa United FC Taraba vs Lobi Stars Gabros FC vs Rangers ? Giwa FC vs Sunshine Stars El-Kanemi Warriors vs Abia Warriors ? Heartland vs Nasarawa United