Bai kamata a ban jan kati ba - Rafa Benitez

Rafa Benitez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan ne karon farko da aka bai wa kociyan jan kati

Kociyan Napoli Rafa Benitez ya ce ya yi mamaki da aka ba shi jan kati a karo na farko kan aikinsa a karawar da suka tashi wasa kunnen doki da Atalanta.

Banitez ya ce "Ba a taba ba ni katin gargadi ba tun lokacin da na fara aikin kociya, saboda haka ban san dalilin da ya sa aka bani jan kati ba".

An kori kociyan ne bayan da ya yi korafi ga alkalin wasa bisa kwallon da Mauricio Pinilla ya ci, a inda alamu suka nuna ya hankade Henrique kafin ya ci kwallon.

Kociyan da ya jagoranci wasanni 600 wanda kuma bai taba karbar katin gargadi ba, ya ce ya kamata a fuskance shi kan fushin da ya yi ba korarsa daga wasan ba."