Mun tada hankalinmu a wasan Barca — Ancelotti

Barcelona Real Madrid Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barcelona tana mataki na daya a teburin La Liga da maki 68

Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya ce salon wasan da suka buga na bayar da kwallo zuwa nesa ne ya sa Barcelona suka doke su 2-1.

Ancelotti ya ce, "A fafatawar farko kafin a tafi hutu mun taka leda, amma bayan da aka dawo daga hutu ba mu saka kaimin da ya kamata ba."

Barcelona ta ci kwallayenta biyu ta hannun Mathieu da Suarez, yayin da Madrid ta farke kwallo ta hannun Ronaldo.

Da wannan nasarar Barca wacce take matsayi na daya a teburin La Liga da maki 68, ta bai wa Real Madrid mai mataki na biyu tazarar maki hudu.